Idan kafafen watsa labaru ba su fadi gaskiya,to wa zai fada? A daidai lokacin da ake watsa shiri na kai tsaye daga tashar talabijin din Iran ta 1, wacce miliyoyin mutane suke kallo, makami mai linzami da aka harbo ya fada akan gininta.Wannan abinda ya faru ba wai kawai ya rusa gini ne, ya binne abinda ake kira ‘yancin tofa albarkacin baki da magana akan gaskiya, sannan kuma uwa uba shi kanshi aikin jarida