HARAJIN WUCEWA

Tambayar da ke ta yawo a cikin kwanakin nan ita ce: a kan wadanne abubuwa ne Iran za ta karbi haraji daga jiragen ruwa masu

Share

Ships crossing a strategic strait under security patrol

1

Tambayar da ke ta yawo a cikin kwanakin nan ita ce: a kan wadanne abubuwa ne Iran za ta karbi haraji daga jiragen ruwa masu ratsawa ta mashigar Hormuz? Yana da kyau mu yi dubi kan batun sosai.

2

Hormuz Mashigar ruwa ce ta kasa da kasa. Amma wani bangare na ruwan yana cikin bangaren kasar Iran ne. Wato jiragen ruwa da ke wucewa ta mashigar dole ne su ratsa ta cikin ruwan kasar Iran.

3

Jiragen ruwa za su iya wucewa ta mashigar bisa sharadin cewa hakan ba zai haifar da matsala ta tsaro ko kuma kawo rashin tsari ga harkokin tashoshin ruwa na kasar ba.

4

Bari mu sake komawa ga tambayrmu ta farko: A kan wadanne abubuwa ne Iran za ta iya karbar haraji daga jiragen ruwa masu ratsawa ta mashigar Hormuz?

5

Amsar a gurguje ita ce: Iran za ta iya karbar haraji daga ayyukan kula da shige da fice na jiragen ruwa, kula da yanayin cunkoson jirage, rakiyarsu domin tsaro, kula da ayyukan gyaransu.

6

Batun gurbatar muhalli saboda shige ta ficen manyan jiragen ruwa ta wannan mashiga shi ma abin dubawa.

7

Haka nan kuma wani da yake da muhimamnci a yi la’akari da shi, shi ne cewa Mashigar Hormuz ba wai kawai hanya ce ta teku ba, wuri ne babban mai tasiri ta fuskacin fitar da makamashi a duniya, a kan haka kula da wurin na bukatar tsari da matakai na musamman.

8

Domin kuwa a kowace shekara kimanin jragen ruwa dubu 20 ne suke ratsawa ta wurin, haka nan kuma sama da kashi 20 cikin dari na na dayen mai da kashi 25 na iskar da ake amfani da su a duniya ta wannan wuri ake fitar da su.

9

Duk da cewa a cikin shekarun baya-bayan nan Iran ta rika yin rakiya ga jiragen ruwa domin basu kariya da tsaro saboda matsalar ‘yan fashin teku.

10

Baya ga haka ma jiragen ruwan Iran masu yin sintiri a cikin ruwa sun sha taimaka ma sauran jirage da kuma kwato su daga hannun ‘yan fashin teku.

11

Iran ita ce take daukar dawainiyar yin hakan don kashin kanta tsawon shekaru, ba tare da ta karbi komai daga wata kasa ko wani kamfani ba, amma yanzu ta sake shawara, bayan da makiyanta suka yi amfani da wannan mashiga wajen kawo mata hari, inda ta shata cewa dole ne a biya ta hakkin duk wata hidima da take yi a wannan mashiga.