Mardhya tana raye; Batun Epstein, bayan fadawar wasu jami’an Turai da na Amurka cikin tarkon Isra’ila!Mardhya tana raye; Batun Epstein, bayan fadawar wasu jami’an Turai da na Amurka cikin tarkon Isra’ila!
Takardu miliyan uku, imel da rahotannin da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta fitar ba wai kawai batun mutane masu aikata laifin badala ba ne, a’a har ma da batun aikin kutse Shin Jeffrey Epstein da Ghislaine Maxwell wakilan cibiyoyin leken asiri na Isra’ila ne?
Sabbin takardu sun bayyana rahotannin sirri na FBI. Takardun sun yi iƙirarin cewa Epstein “wakilin haɗin gwiwa ne na Mossad”
kuma tsohon Firayim Ministan Isra’ila Ehud Barak ya horar da shi a matsayin wakilin leken asiri. Haka nan kuma takardar ta nuna alaka da hadin gwiwa tare da iyalan Maxwell. Kuma takardar ta yi nuni da abubuwa masu matukar hadari.
Takardu sun nuna cewa Epstein ya ci gaba da tuntuɓar Barak bayan an yanke masa hukunci a shekarar 2008, kuma sunan Barak ya bayyana sau 4,000 a cikin takardun Epstein.
Wannan ba kawai wani abu ne na yau da kullun ba; sun yi aiki tare kan harkokin tsaro da leƙen asiri na ƙasashen waje.
Epstein ya shirya tarurruka a asirce tsakanin Barak da jami’an Rasha a lokacin yakin Siriya. Domin tilasta wa Bashar al-Assad ya ja da baya.
Ya kuma ƙarfafa Barak a cikin wani sauti da aka nada don yin aiki tare da wani kamfanin fasaha da sa ido mai suna Palantir, wanda daga baya ya zama babban bangare a cikin rundunar soji da leƙen asiri ta Isra’ila.
Takardun sun kuma nuna cewa Barack da wani da ake zargi da leƙen asiri sun zauna a gidan Epstein da ke New York na dogon lokaci.
A daidai da mutumin da aka yanke wa hukuncin laifin fyade yake tsare, a lokaci guda kuma yana ajiye jami’an leƙen asiri a gidansa,
kuma ya ci gaba da yin wasiƙu akai-akai da ‘yan siyasa da jami’an ƙasashen waje, kuma ya shiga tsakani a yarjejeniyoyi na ƙasashen duniya, tabbas hakan ya nuna akwai lauje cikin nadi.