Miliyoyin Iraniyawa sun kunyata makiya tare da dakile markircinsu ga juyin juya hali

Miliyoyin mutanen Tehran sun cika titunan babban birnin kasar Iran domin nuna kin amincewa da tashe-tashen hankulan da 'yan koren Amurka da 'yan sahyoniya su

Share

Miliyoyin mutanen Tehran sun cika titunan babban birnin kasar Iran domin nuna kin amincewa da tashe-tashen hankulan da 'yan koren Amurka da 'yan sahyoniya su ka haddasa a cikin kasar.

Miliyoyin mutanen Tehran sun cika titunan babban birnin kasar Iran domin nuna kin amincewa da tashe-tashen hankulan da ‘yan koren Amurka da ‘yan sahyoniya su ka haddasa a cikin kasar. A birnin Tehran iraniayawan sun cika dandalin “inqilab” da dukkanin titunan da suke zagaye da shi, na kusa da nesa, saboda tabbatar da cewa su al’umma daya ce, wacce ba za ta bari abokan gaba na waje su yi tasiri a cikinta ba