1
Me yasa tsagaita wuta a Yammacin Asiya ba yana nufin dakatar da yaki ne ba, yana nufin ci gaba da yakin ne bayan wani dan lokaci na dakatar da shi?
2
Kuma me yasa Iran ta sanar da cewa tana da gab da sake da sake bude wuta?
3
Bayanan da suke fitowa a hukumance sun ce tsagaita wuta ne na tsawon makonni biyu, amma bayanai sun nuna akasin haka.
4
A cewar Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon, a hare-haren ranar 8 ga Afrilu kaɗai, Isra’ila ta kai hari kan wurare sama da 160, inda ta kashe aƙalla mutane 89 tare da raunata sama da 700.
5
Matsalar ba ta yau ce kawai ba. Ana fuskantar wani mawuyacin yanayi. A yakin Gaza, an karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau da yawa.
6
Ko a yarjejeniyar ƙarshe, a daidai lokacin da aka sanar da kawo ƙarshen rikicin, an ci gaba da kai hare-haren bam, mashigar Rafah ta kasance a rufe. Wanda hakan yana nufin yarjejeniya ce kawai a kan takarda.
7
Yanzu bari mu koma zuwa watan Yuni shekara ta 2025.
8
Isra’ila da Amurka sun kai hari na hadin gwiwa, an kai hare-hare a tashoshin nukiliya na Iran, kuma an kashe masana kimiyya da mutane ‘yan ƙasar Iran.
9
An ayyana tsagaita wuta bayan kwana 12. Amma a watan Maris na 2026, an sake maimaita irin wancan abin da ya faru:
10
Kisan gilla da aka yi da gangan ta hanyar hare-haren da aka shirya, da kuma kashe jami’ai da ‘yan ƙasa.
11
Bayanan da ke fitowa daga Lebanon sun tabbatar da haka.
12
Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka yi a baya ba taɓa kawo karshen hare-haren jiragen sama marasa matuƙa ba, kisan gilla a yankunan da ke kan iyakar kudancin kasar, da kuma jefa bama-bamai a yankunan kudancin Bekaa.
13
Wato tsagaita wuta ya fi zama hanya ta canja dubarun yaki da sake shiri a kan dakatar da yaki baki daya, saboda wannan dalili Iran ta ce tana a shirye domin tunkarar kowane irin yanayi.
14
Idan aka maimaita abin da aka yi na karya yarjejeniyoyin baya, an kawo karshen duk wani batu na dakatar da bude wuta.
15
A daga bangaren kuma akwai wani batu wanda ya kunshi wata manufa mafi girma da hadari, wanda ya samu wurin zama a cikin kwakwalen ‘yan siyasa a Isra’ila da ma wasu kasashen yamma:
16
Shi ne Faɗaɗa tasirin mamaya a daukacin yankin, a ƙarƙashin hujjar kafa “Isra’ila Babba.”
17
A bisa wannan mahanga, ba su yin la’akari da duk wata yarjejeniya ta tsagaita bude wuta na din-din-din, domin samun hujjar komawa yaki a duk lokacin da suka dama.