Ministan harkokin wajen Rasha ya taya Ministan Harkokin Waje Seyyed Abbas Araqchi murnar zagayowar ranar nasarar juyin juya halin Musulunci da kuma Ranar Kasa ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wani bangare na sakon taya murna da Sergei Lavrov ya aikewa Araghchi ya ce: “Ina matukar farin ciki da ci gaban da aka samu na hadin gwiwar dabaru tsakanin Iran da Rasha, wanda ya dogara ne kan girmama juna, amincewa, da kuma la’akari da muradun juna.”
Ya kara da cewa: “Ina ganin cewa huldar diflomasiyya da hadin kai tsakanin kasashen biyu muhimmin abu ne ga kwanciyar hankali da tsaro a yankin kuma zai taimaka sosai wajen bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu.”
Gwamnatocin kasashen duniya da dama sun aike da irin wadannans akonni ga gwamnatin kasar Iran, da hakan ya hada da kasashen Asia, Afirka da kuma na Latin Amurka.