Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana cikakkun bayanai game da tattaunawan Putin da Trump
Mataimakin shugaban kasar Rasha Yuri Ushakov ya sanar da wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban Amurka Donald Trump a wasu ‘yan sa’o’i da suka gabata.
Ushakov ya ce: “A wasu ‘yan sa’o’i da suka gabata, bisa jagorancin shugaban Amurka Donald Trump, an yi wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin Trump da Putin,” yana mai cewa: “Tattaunawar ta dauki kusan mintuna 40.”
Ya kara da cewa: Trump ya yiwa Putin bayanin sakamakon tattaunawarsa da shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky da shugabannin kasashen Turai. Ya lura cewa tattaunawa tsakanin Putin da Trump ta kasance “ta gaskiya kuma mai ma’ana.”
Ushakov ya ce, a yayin tattaunawar, shugabannin kasar Rasha Vladimir Putin da Donald Trump sun bayyana goyon bayansu ga ci gaba da yin shawarwari kai tsaye tsakanin tawagogin Rasha da Ukraine.
Ya kara da cewa: “Sun amince da ci gaba da tuntubar juna dangane da Ukraine da sauran batutuwa masu muhimmanci kan ajandar kasa da kasa da kasashen biyu.”
Ushakov ya ce: “Shugaban na Rasha ya sake jaddada muhimmancin kokarin da Donald Trump ke yi da kansa na samar da mafita da za ta kai ga cimma matsaya na dogon lokaci a Ukraine.”