Kasar Rasha ta sake gargadin kasashen dake kokarin bai wa Ukarine makamai.
Rasha ta yi wannan gargadin ne a daidai lokacin da ta karbi shugabancin kwamitin tsaro na MDD na wannan watan Yuli.
Vassily Nebenzya, wakilin Rasha a MDD, ya bayyana gataron taron ‘yan jarida cewa : duk wani mataki na bai wa Ukraine makamai ba zai haifar da ‘da mai ido ba, sannan kuma zai fuskanci mayar da martini na siyasa inji shi.
Kuma a cewar a kwana da sanin cewa za’a lalata dukkan makamman, kamar yadda aka lalata na kasashen yamma da Amurka.
Jakadan na Rasha a MDD, ya kuma tabo batutuwa da dama inda ya bukaci a kawo sauye-sauye a kwamitin tsaro na MDD, saboda rashin adalci da ake nunawa musamman ga Afrika, wacce ba ta da wakilci sosai a kwamitin sulhu idan akayi la’akari da kasashen yammacin duniya da sukayi kane-kane a kwamitin.
Vassily Nebenzya, ya bayyyan ajandar kwamitin tsaron MDD na wannan watan Yuli, inda za’a gudanar da manyan taruka guda uku game da huldar kasa da kasa a bias tsari na cin moriyar juna da adalci a ranar 16 ga wata, sai kuma wata muhawara a game da warware rikici a Gabas ta Tsakiya wacce ministan harkokin wajen kasar Sergueï Lavrov, zai jagoranta a ranar 17 ga watan Yuli.