Jakadan kasar Rasha na din din din a cibiyoyin MDD da suke Vienna, ya bayyana cewa dakatar da aiwatar da yarjeniyar shirin Nukliya na kasar Iran wanda ake kira JCPOA, wacce kuma aka samar da shi a shekara ta 2015, da kasashen yamma suka yi, shi ne ya haddasa dukkan matsalolin da suka biyo baya.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto, Mikhail Awliyonov yana fadar haka a hirar da ta hada shi da jaridar Ezustiyo na kasar Rasha.
Jakadan ya kara da cewa a tsakanin shekara ta 2021 da kuma 2022 an tattauna da kasashen yamma kan yadda za’a aiwatar da yarjeniyar JCPOA da kasashen bayan da kasar Amurka ta fice daga yarjeniyar a shekara ta 2018, amma sai kasashen yamma suka yi watsi da ita sannan suka dorawa kasar Iran sabbin takunkuman tattalin arziki. Jakadan ya kuma kara da cewa a halin yanzu ba za’a warware wadannan matsalolin da suke tasowa kan shirin Nukliyar kasar Iran ba, sai an dawo kan yarjejeniyar ta JCPOA, sannan wadannan kasashen su mayarwa Iran hakkokinta da suka take a cikinta, wadanda suka kaita ga maida martanin da ta yi.
Ya ce, a halin yanzu shekaru ukku sun gabata da yin watsi da yarjeniyar, sannan har yanzun kasar Iran bada sabawa yarjeniyar ba, wanda ya kai ga yarjeniyar zata mutu a cikin watan Octoban shekara ta 2025 da muke ciki. Jakadan ya ce har yanzun ba’a da wani abu da zai maye gurbin yarjeniyar ta JCPOA. Wanda ke samun goyon bayan kudurin kwamitin tsaro na MDD mai lamba 2231.