Rahotonni suna karyata da’awar ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi game da halin da ake ciki a birnin Halab na kasar Siriya
Kafofin watsa labarai da shafukan sada zumunta sun wallafa faifan bidiyo da suke karyata labaran da ‘yan ta’adda masu kafirta musulmi suke yadawa game da birnin Halab na kasar Siriya tare da tabbatar da cewa abin da ya faru ba komai ba ne illa yakin yada labarai da farfagandar karya.
Farfagandar tana zuwa ne a daidai lokacin da sojojin kasar Siriya suka tabbatar da yin mummunar barna ga ‘yan ta’adda tare da tarwatsa ‘yan ta’addan a birnin Halab, kafofin yada labaran da ke da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda sun yi ikirarin cewa ‘yan ta’adda sun isa tsakiyar birnin Halab ta hanyar mamaye wasu yankuna da suke shiyar yammacin kasar.
Wannan dai yana zuwa ne a daidai lokacin da kafafen yada labaran da suke da alaka da wadannan gurbatattun kungiyoyi ke ikirarin samun ci gaban ‘yan ta’adda a kan wasu yankuna na biranen Halab da Idlib.