Sakatare Janar na kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sheikh Naim Qasem ya ce gwamnatin Lebanon ce ke da alhakin tabbatar da cewa Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar tsagaita bude wuta a kasar ta Lebanon.
“Gwamnatin Lebanon, bayan tsawaita yarjejeniyar tsagaita bude wuta, ita ce ke da alhakin bibiyar lamarin da kuma matsa lamba kan kasashe masu sa ido da masu shiga tsakani don dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kaiwa da keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta,” in ji shi a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin dazu.
Sheik Qasem ya ce kungiyar Hizbullah na taka-tsan-tsan don bai wa gwamnatin Lebanon damar sauke nauyin da ya rataya a wuyanta karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Faransa da Amurka suka shiga tsakani a ranar 27 ga watan Nuwamba.
Ya yi gargadin cewa Isra’ila na ci gaba da karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Ya kamata Isra’ila ta janye dukkan sojojinta daga Lebanon a ranar 26 ga watan Janairu a karkashin yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta rattabawa hannu da kungiyar Hizbullah a watan Nuwamba.
Sai dai kuma ta ki yin hakan, inda aka tsawaita wa’adin zuwa ranar 18 ga watan Fabrairu.
Sama da ‘yan kasar Lebanon 80 ne kuma aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa kasar tun bayan da yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki.