Putin Ya Taya Masoud Pezeshkian Murnar Lashe Zaben Iran

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya taya Masoud Pezeshkian murnar lashe zaben shugabancin kasar Iran Fadar Kremlin ta bayyana a ranar Asabar cewa shugaban Putin

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya taya Masoud Pezeshkian murnar lashe zaben shugabancin kasar Iran

Fadar Kremlin ta bayyana a ranar Asabar cewa shugaban Putin yana mai fatan inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni, don amfanin al’ummominmu ta fuskar tsaro da zaman lafiya a yankin.”

Vladimir Putin ya bayyana cewa, alakar da ke tsakanin Rasha da Iran abu ne na abokantaka kuma ta ginu bisa kyakkyawar alaka ta makwabtaka.

Bangarorin biyu a cewarsa sun hada kai don magance matsalolin kasa da kasa yadda ya kamata, “in ji shi.

Pezeshkian ya lashe zaben da aka yi a jiya Juma’a, da kashi sama da 53,66% na jimillar kuri’un da aka kada a yayin da abokin hamayarsa Saeed Jalili ya samu kashi 44.34%  na kuri’un.

Hedikwatar tsara zaben kasar ta ce sama da kasha 50% na wadanda suka cancanci zabe ne suka fito kada kuri’a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

An kira zaben ne da wuri sakamakon rasuwar shugaban kasar Ebrahim Ra’isi a wani mummunan hastarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayu da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments