Putin ya gayyaci Pezeshkian zuwa babban taron BRICS

Jakadan kasar Iran a kasar Rasha ya sanar da cewa shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Rasha a gefen taron shugabannin kasashen BRICS

Jakadan kasar Iran a kasar Rasha ya sanar da cewa shugaban kasar Iran zai gana da shugaban kasar Rasha a gefen taron shugabannin kasashen BRICS a birnin Kazan na kasar Rasha.

Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Rasha Kazem Jalali, a wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na “Tass” ya bayyana cewa, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai halarci taron kasashen BRICS da za a yi a Kazan, inda zai gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Dangane da haka, Jalali ya ce: Ina ganin shugaban zai halarci taron BRICS da za a yi a Kazan. A halin yanzu muna shirye-shiryen wannan tafiya don zama mai fa’ida da nasara ga dangantakar Iran da Rasha.

Ya kara da cewa: Dangane da alakar da ke tsakanin kasashen biyu, ana shirin yin ganawa tsakanin shugabannin Rasha da Vladimir Putin, da na Iran Masud Pezeshkian, kamar yadda kuma za a yi wasu tarukan ganawar bayan fage tsakanin shugaban na Iran da k7uma shugabannin wasu kasashe a wannan taro.

Har ila yau, a cikin wannan hirar, yayin da yake amsa tambayar ko za a iya sanya hannu kan cikakkiyar yarjejeniya tsakanin kasashen biyu a taron kasashen BRICS a birnin Kazan, jakadan na Iran ya ce: Mun tattauna da takwarorinmu na Rasha game da hakan, a hakikanin gaskiya wannan shi ne na farko,  Ban da haka kuma, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ne zai kasance mai masaukin baki, kuma wannan ita ce ziyarar farko da shugaban kasar Iran Masoud Mezkiyan zai kai kasar Rasha a hukuamnce.

Jalali ya kara da cewa: A gaskiya mun kammala dukkanin tsare-tsaren yarjejejniyar mai suna (comprehensive strategic documents) tsakanin Iran da Rasha, wadda kuma ake sa ran za a rattaba hannu a kanta tsakanin kasashen biyu a ziyarar shugaba Pezeshkian a Rasha.

Rasha ta karbi ragamar shugabancin BRICS a ranar 1 ga Janairu, 2024, kuma za ta ci gaba har zuwa karshen wannan shekara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments