Pourmohammadi Ya Bukaci Musulmi Su Hada Kai Domin Goyon Bayan Gaza

Mostafa Pourmohammadi, dan takara a zaben shugaban kasar Iran da ke tafe, ya yi kira da a hada kai a tsakanin musulmi domin goyon bayan

Mostafa Pourmohammadi, dan takara a zaben shugaban kasar Iran da ke tafe, ya yi kira da a hada kai a tsakanin musulmi domin goyon bayan al’ummar Palastinu, musamman ma wadanda ake zalunta a zirin Gaza.

Pourmohammadi, tsohon ministan harkokin cikin gida da shari’a ya bayyana hakan yayin wata hira da kafar yada labarai ta al-Alam a ranar Laraba.

Ya kuma jaddada wajabcin dawo da martaba da daukakar duniyar musulmi, tare da yin kira da a ba da hadin kai wajen goyon bayan Falastinawa.

Pourmohammadi ya ce, “Mu hada karfi da karfe don kare hakkin juna da karfafa alakar ‘yan uwanmu, da raya muradunmu na bai daya, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali,” in ji Pourmohammadi.

Ya kara da cewa: “Ya kamata mu tashi tsaye wajen yaki da makiya, mu kuma yi aiki domin kare al’ummar Palastinu da ake zalunta da kuma al’ummar Gaza da kuma dawo da daukaka ga kasashen musulminmu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments