Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Iran zata iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Iran a yau, kamar irin abubuwan da ta faru a baya, za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen gina duniya da ba ta da tashin hankali, da kuma cike da zaman lafiya, da abota, da zaman tare, da tattaunawa, kuma za ta iya sanya tausayi ya mamaye harshen bai daya ta hanyar yin amfani da arzikin al’adu.
A cikin sakon da ya gabatar a wurin taron karrama mawakan Iran Shams Tabrizi da Mawlana Jalaluddin Mohammad Balkhi, shugaba Pezeshkian ya ce a ranar Talata: An ambaci ranakun 29 da 30 ga watan Satumba a cikin kalandar kasar Iran sunayen manyan masana ilimi da ruhi guda biyu Shams Tabrizi da Mawlana Jalaluddin Mohammad Balkhi da suke wakiltar dama mai kima da gado mai wanzuwa a wakokinsu da suke fayyace dabi’ar dan Adamataka da zurfin ilimummuka ga dukkan bil’adama.”
Pezeshkian ya kara da cewa: A tsawon tarihi, al’adar Iran ta kasance matattarar taurari masu haskakawa irin wadannan; manyan mutane wadanda suka share fagen samun hadin kai da zaman lafiya a duniya tare da harshen wakoki da sufanci, tare da mahangar hikima, gami da ma’anar soyayya da abokantaka. Abin da aka gada daga Shams Tabrizi da Mawlana Jalal al-Din bai takaitu ga Iran da Iraniyawa kadai ba, a’a ya shafi dukkan al’ummomin da ke makwabtaka da duniya da kuma duniyar bil’adama.