Pezeshkian : Inganta Rayuwar Jama’a Na Daga Cikin Manyan Abubuwan Da Na Sa A Gaba

Masoud Pezeshkian, daya daga cikin ‘yan takara shida a zaben shugaban kasar da za a yi ranar 28 ga watan Yuni, ya ce baya adawa

Masoud Pezeshkian, daya daga cikin ‘yan takara shida a zaben shugaban kasar da za a yi ranar 28 ga watan Yuni, ya ce baya adawa da diflomasiyya da tattaunawa amma ba zai yi kasa a gwiwa ba.

Pezeshkian, wanda tsohon ministan lafiya ne kuma gogaggen dan majalisa wanda kuma a baya ya taba rike mukamin mataimakin kakakin majalisar, ya bayyana hakan ne a wani shirin gidan talabijin na kasar a ranar Talata, yayin da yake bayyana manufofinsa na ketare idan ya zama shugaban kasa.

“Diflomasiyya da tattaunawa ba su kai wulakanci ba. Ba za mu yi fada da kowa ba, sai dai in sun so su cutar da martaba da girman kasarmu.

Dan takarar shugaban kasar ya ci gaba da cewa, inganta rayuwar jama’a na daga cikin manyan abubuwan da ya sa a gaba, yayin da ya jaddada cewa manufofin kasashen waje na da matukar tasiri ga rayuwar jama’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments