Pezeshkian: Dole Ne Kungiyar Hadin Gwiwar Shanghai Ta Zama Hanyar Sanar Da Zaman Lafiya A Duniya

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta dauki matakai wajen samar da duniya mai zaman lafiya Shugaban kasar Iran

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kungiyar hadin gwiwar Shanghai ta dauki matakai wajen samar da duniya mai zaman lafiya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi imanin cewa, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a matsayin muhimmin ginshiki na tsarin kasa da kasa, dole ne ta dauki matakai na zahiri, na musamman, da kuma a bayyane kan hanyoyi guda biyu masu kamanceceniya da juna, don samar da duniya mai zaman lafiya, da duniya mai shirin fadada hadin gwiwar tattalin arziki.

A yayin taron kolin shugabannin kungiyar hadin gwiwar Shaghai “SCO” karo na 25 a birnin Tianjin na kasar China, shugaba Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, a cikin tsarin karfafa hadin gwiwar hada-hadar kudi don rage tasirin takunkumin karya doka kan huldar tattalin arziki tsakanin mambobin kungiyar, Iran ta ba da shawarar karfafa shawarar “Asusun SCO na musamman da matsuguni” a matsayin wata hanya mai amfani ta inganta hadin gwiwar hada-hadar kudi. Ya kara da cewa, wannan shiri ya ta’allaka ne kan manyan matakai uku: fadada matsuguni a cikin kudaden kasa da rage dogaro da dala a musayar mambobi; ƙaddamar da hanyoyin haɗin gwiwa na dijital da kuma amfani da kuɗin dijital na babban banki don aminci da biyan kuɗi mai sauri; da kuma kafa asusun musanya kudin waje don tallafawa kasashen da suka fuskanci matsin lamba ko rikicin kudi.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments