Pezeshkian: Dangantakar Iran da Rasha za ta ci gaba da habaka bisa manufofi masu dorewa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce dangantakar da ke tsakanin Iran da Rasha za ta ci gaba da fadada bisa manufofi masu dorewa. Pezeshkian

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce dangantakar da ke tsakanin Iran da Rasha za ta ci gaba da fadada bisa manufofi masu dorewa.

Pezeshkian ya ce, habaka hadin gwiwa tsakanin Tehran da Moscow zai gurgunta tasirin takunkumai da kuma ayyukan rashin adalci da ake yi wa kasashen biyu.

Pezeshkian ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da sakataren kwamitin tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu a Tehran babban birnin kasar Iran, inda ya jaddada tarihin dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu da cewa ta tarihi ce.

Yayin da yake ishara da kalaman Shoigu game da shirye-shiryen ganawar da shugabannin kasashen biyu za su yi a gefen taron kasashen BRICS da za a yi a Kazan, Pezeshkian ya bayyana fatan cewa, irin wannan ganawar za ta kai ga kara samun kyakkyawar yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, shiyya-shiyya, da kuma kasa da kasa a tsakanin Iran da Rasha, da hakan ya hada da tsarin yarjeniyoyi na BRICS, Shanghai, da kuma Eurasian.

A nasa bangaren, Shoigu ya jaddada cewa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bukace shi da ya isar wa manyan jami’an kasar Iran cewa, matsayin Rasha kan hadin gwiwa da Iran kan batutuwan yankin na nan daram bai canja ba.

“Putin yana fatan ganawa da ku a gefen taron kasashen BRICS da za a yi a birnin Kazan na kasar Rasha,” in ji Shoigu ga Pezeshkian.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments