Pezeshkian Da Guterres Sun Tattauna Kan Halin Da Ake Ciki A Gabas Ta Tsakiya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana matukar damuwar kasarsa dangane da karuwar tashe-tashen hankula a gabas ta tsakiya, sakamakon ayyukan ta’addanci da Isra’ila ke

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana matukar damuwar kasarsa dangane da karuwar tashe-tashen hankula a gabas ta tsakiya, sakamakon ayyukan ta’addanci da Isra’ila ke aikatawa.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a birnin New York na kasar Amurka a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79.

Pezeshkian ya ce a ranar farko ta shugabancinsa Isra’ila ta kashe Ismail Haniyeh shugaban siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a birnin Tehran babban birnin kasar Iran.

Ya kara da cewa gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kashe Falasdinawa sama da 41,400 a yakin da ta ke yi na kisan kare dangi a zirin Gaza, kuma a halin yanzu ta fadada yakin nata  zuwa kasar Labanon, inda ta kashe mutane da dama.

Ya ci gaba da cewa, “Mun damu matuka game da yaduwar rikicin a fadin yankin.”

Shugaban na Iran ya kuma jinjina wa Guterres kan yadda ya nuna juyayinsa da damuwarsa dangane da mummunan fashewar mahakar kwal da ta auku a gabashin kasar Iran.

Pezeshkian ya kara jaddada cewa Iran na neman samar da zaman lafiya da tsaro mai dorewa a yammacin Asiya tare da taimakon gwamnatocin kasashen da ke makwabtaka da ita ciki har da kasashen yankin tekun Fasha.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments