Gwamnatin kasar Pakistan ta ce da akwai hannuwan Afghanistan da kuma India a garkuwa da jirgin kasa na soja da aka yi a cikin kasar a ranar 13 ga watan Maris,wanda ya jefa mutanen kasar cikin damuwa akan batun tsaro.
Mahukuntan kasar ta Pakistan sun kuma ce; Binciken farko ya tabbatar da cewa wasu masu dauke da makamai ne su ka yi garkuwa da jirgin kasar, da sun shigo ne daga iyakarAfghanistan sai kuma wani dan India wanda ya shiya yadda za a yi.
Gwamnatin kasar ta Pakistan ta sanar da tsananta matakan tsaro domin kame wadanda su ka yi garkuwa da jirgin da kuma daukar matakan hana, irin haka faruwa a nan gaba.
Ya zuwa yanzu babu wata kungiyar da ta fito fili ta dauki alhakin abinda ya faru.
Gwamnatin kasar ta Pakistan ta ce, da akwai masu dauke makamai da sun kai 50 da suke garkuwa da jirgin kasan. Ya zuwa yanzu dai mutane 31 ne su ka rasa rayukansu da sun kunshi jami’an tsaro da kuma fararen hula.
A cikin shekarun bayan nan alaka a tsakanin Pakistan da Afghanistan ta kara kamari.