Pakistan Ta Soki Amurka Akan Yadda Take Kokarin Kawo Cikas A Shirin Hadin Gwiwa Na  Shimfida Bututun Gas Da Iran

Shugaban kungiyar “Jama’at-Islami” na kasar Pakistan Liyaqat Baluch wanda ya yi suka akan yadda Amurka take matsin lamba da zummar dakatar da shimfida bututun iskar

Shugaban kungiyar “Jama’at-Islami” na kasar Pakistan Liyaqat Baluch wanda ya yi suka akan yadda Amurka take matsin lamba da zummar dakatar da shimfida bututun iskar Gas a tsakanin Iran da kasar Pakistan.

Liyaqat Baluch ya ce, Amurka tana son yi wa shirin kafar angulu ne duk da cewa  aiwatar da shi zai kyautata rayuwar mutanen Pakistan.

Wani sahe na bayanin shugaban  kungiyar ‘Jama’atu-Islami’ ya kunshi cewa; Abinda Amurka take yi a cikin wannan yankin shi ne hada fadace-fadace da tatar da rikici, daga cikin hard a yadda take goyon bayan laifukan yakin HKI akan al’ummar Gaza.

A makon da ya shude ma dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen Pakistan ya mayar wa da Amurka martani akan shimfida bututun Iskar Gas din na Iran, yana mai cewa, matsayar kasarsa akan wannan batu a ifli take.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments