Nijar : Yau Juma’a Za’ayi Jana’izar Mirigayi Hama Amadou

A Nijar idan an jima ne za’ayi jana’izar tsohon fira ministan kasar Mirigayi Hama Amadou wanda Allah ya yi wa rasuwa A cikin daren ranar

A Nijar idan an jima ne za’ayi jana’izar tsohon fira ministan kasar Mirigayi Hama Amadou wanda Allah ya yi wa rasuwa A cikin daren ranar Laraba.

Hama Amadou ya rasu a lokacin da yake da shekaru 74 da haihuwa, bayan ya yi fama da rashin lafiya. 

A yau juma’a ne za’ayi bikin girmama mamacin a fadar shugaban kasa, kafin a dauki gawarsa zuwa kauyen Youri inda za’a jana’izarsa.

An bayyana mirigayin a matsayin gawurtaccen dan siyasa, wanda ya sha gwagwarmaya domin ’yancin kasar Nijar, da tabbatar da tsarin demokaradiyya na-gari.

Jama’ar kasar a sahun gaba ‘yan siyasar na ta aikewa da sakon ta’aziyya tare da bayyana shi dan siyasa marar misaltuwa a kasar.

Gwarzon dan siyasar Nijar tun lokacin shugaba Seyni Kountche zuwa shugaba Tandja Mamadou, Hama Amadou ya rike manyan mukamai da suka hada da kasancewa faraminista a shekarar 1995, kana shugaban majalisar dokoki duk a lokacin mulkin shugaban kasa Tandja Mamadou.

Bayan ficewa daga jam’iyyar MNSD-Nasara, Hama Amadou ya kafa jam’iyyarsa ta Modem FA Lumana Afrika.

An haifi Hama Amadou a ranar 3 ga watan Maris din shekarar 1950 a kauyen Youri, yankin Tillabery.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments