Nigeria: Zazzabin “Lassa” Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 118 Tun Farkon Wannan Shekara

Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su

Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025.

A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a cikin jahoji 33 na fadin kasar, kuma bincike da aka yi akan wadanda ake tsammanin ta kama, ya tabbatar da cewa an sami mutane 645 da su ka kamu da ita.

Ita dai wannan cutar mai yaduwa a Nigeria, ana kamuwa da ita ne ta hanyar cudanya a tsakanin mutane ko kuma taba kayan gida da su ka gurbana daga bahaya ko fitsari na mutane da su ka kamu da ita.

Tare da cewa an dauki shekara da shekaru ana fama da wannan cutar a cikin kasar ta Nigeria, sai dai har yanzu babu wani ci gaba na azo a gani da aka samu na dakile wannan cuta, saboda halayyar kazanta da rashin muhalli mai tsafta.

Ana samu wadanda suke tsira daga cutar amma a lokaci daya tana kisa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments