Nebenzia : Hare-haren Sojojin Isra’ila a Lebanon da Syria na kara dagula lamura a yankin

Wakilin kasar Rasha na Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzia ya bayyana cewa, Harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan Syria da Lebanon, abubuwa ne

Wakilin kasar Rasha na Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzia ya bayyana cewa, Harin baya-bayan nan da Isra’ila ta kai kan Syria da Lebanon, abubuwa ne da ke kara dagula zaman lafiya a yankin.

A yayin da yake jawabi ga Majalisar Dinkin Duniya, Nebenzia ya ce “daya daga cikin abubuwan da ke nuni da yunkurin dagula zaman lafiya a yankin shi ne yadda Isra’ila ke ci gaba da mamaye yankin Golan na klasar Syria.”

Sauran abubuwan da ke haifar da rashin zaman lafiya, a cewar wakilin Majalisar Dinkin Duniya, su ne yadda “Isra’ila” ke hana ‘yan kasar Lebanon da suka rasa matsugunansu komawa gidajensu a Kudancin kasar, da kuma ayyukan tada hankali da ta yi ta hanyar kai farmakin soji a lokacin jana’izar Sayyed Hassan Nasrallah a wasu yankuna na kudancin kasar ta Lebanon.

Jakadan ya yi Allah wadai da hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila” ta kai a baya-bayan nan a Lebanon da Siriya musamman bayan da Haaretz ta fitar da hotunan tauraron dan adam da ke fallasa shirye-shiryen sojojin mamaya na Isra’ila a kan iyakar Siriya.

Hotunan sun bayyana cewa, Isra’ila ta kafa sabbin sansanonin soji kimanin guda bakawai, tun daga Dutsen Hermon da ke arewacin yankin da ta  kwace tsakanin Siriya da yankunan Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments