NBS: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya Ya Karu Zuwa Kashi 34.19

Rahoton Hukumar (NBS), ya bayyana cewar hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.19 a watan Yuni. Wannan ya nuna ƙaruwar hauhawar farashi sosai idan

Rahoton Hukumar (NBS), ya bayyana cewar hauhawar farashin kayayyaki ya ƙaru zuwa kashi 34.19 a watan Yuni.

Wannan ya nuna ƙaruwar hauhawar farashi sosai idan aka kwatanta da watannin baya.

Kazalika, farashin kayan abinci ya ƙaru sosai, inda ya kai kashi 40.87, idan aka kwatanta da kashi 25.25 da aka samu a watan Yuni 2023.

Wannan na zuwa ne bayan ƙarin da ake samu kan farashin kayan abinci na yau da kullum kamar gero, doya, man gyada, busashen kifi da sauran kayan masarufi.

Rahoton ya bayyana cewa hauhawar farashi na shekara-shekara ya ƙaru da maki 11.40 daga watan Yuni 2023, wanda ya ƙaru zuwa kashi 22.79.

Har wa yau, yawan hauhawar farashin kayayyaki wata-wata a watan Yuni 2024 ya kai kashi 2.31, wanda hakan ya fi na watan Mayu 2024, inda aka samu kashi 2.14.

A jihohin Bauchi, Kogi, da Oyo sun fuskanci girman hauhawar farashin kayayyaki na shekara-shekara, yayin da Borno, Benuwe da Katsina suka kasance inda aka samu hauhawar farashi kaɗan.

A bayanan wata-wata kuwa, Yobe, Abuja, da Ondo sun samu fuskanci girman ƙaruwar hauhawar farashi, yayin da Nasarawa, Osun, da Kano suka kasance inda aka samu hauhawar farashin kayayyaki mara yawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments