Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ya bayyana cewa, marigayi shugaban kasar Iran Ibrahim Raeisi mutum ne mai cikakken imani a fagen siyasar Falasdinu da kuma fafutukar ‘yan gwagwarmaya a yankin.
Sayyid Hasan Nasrallah ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a birnin Beirut na kasar Labanon domin nuna girmamawa ga shugaban kasar da mukarrabansa da suka yi shahada a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a arewa maso yammacin kasar Iran.
Nasrallah ya kuma kira ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian, wanda shi ma ya yi shahada a cikin lamarin da cewa, “mai imani ne da batun gwagwarmaya da yunkurinta.”
Shugaban na Hizbullah ya bayyana wannan lamari a matsayin mai matukar raɗaɗi da bakin ciki a ciki da wajen kasar Iran.
Ya yi nuni da cewa miliyoyin mutane ne suka halarci jana’izar shahidan a fadin Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Sayyid Nasrallah yayin da yake ishara da taron jana’izar marigayi Raisi ya ce: Taron jana’izar shi ne na uku mafi girma a tarihi, bayan taron jana’izar Imam Khumaini da kuma Shahid Qassem Soleimani.