Nasarallah: HKI Ta Kai Hare Hare Kan Fararen Hula Da Gangan A Kudancin Birnin Beirut Don Kauda Hankali Daga Batun Kisan Majdal-Shams

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah, a jawabin da ya gabatar a yammacin yau Alhamis, a lokacinda ake jana’izar Fuad Shukr, wani

Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon Sayyid Hassan Nasarallah, a jawabin da ya gabatar a yammacin yau Alhamis, a lokacinda ake jana’izar Fuad Shukr, wani babban kwamandan kungiyar a birnin Berut, da kuma dangane da kissan da HKI ta yi wa shugaban kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a jiya Laraba a birnin Tehran, ya bayyana cewa sojojin yahudawan da gangan suke kai hare hare kan fararen hula da sunan daukar fansa kan shuwagabannin kungiyoyi masu gwagwarmaya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Sayyid Nasarrallah, ya na cewa kungiyarsa ta musanta cewa tana da hannu a hare-haren  Majdal-Shams na yakin tuddan Golan na kasar Siriya, inda mafi yawan wadanda aka kashe mata da yara ne. Ya kuma kara da cewa, manufar hare-haren Majdal-Shams, ita ce hada rigima tsakanin Mabiya mazhabar shia da Durus, wadanda suke rayuwa tare a tuddan Golan na kasar ta Siriya.

Ya kara da cewa: Tun farko mun rika mun barranta kammu da kai hare-hare a tuddan Golan, sai dai, idan har mune muka kai, ko da, da kuskure ne, muna da jaruntar fadar hakan, inji Sayyid Nasarallah.

Shugaban kungiyar Hizbullah ya kammala da cewa, mun rika mun sa kammu don tallafawa Falasdinawa a Gaza, kuma zamu ci gaba da hakan har zuwa lokacinda za’a  dakatar da yaki  a can.

Sannan ga wadanda suke kira garemu, kan kada mu rama hare haren da aka kai mana, a kudancin birnin Beirut kuma, sai Nasarllah y ace: ta yaya hakan zai kasanshen? Muna cikin yaki ko ta ina? Yace: Yanzun ta yaya JMI zata kasa yin wani abu bayan an kashe bakonta a cikin kasarta.?

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments