A wani bangare na sauya majalisar ministocinsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rushe Ma’aikatar Bunkasa Ci-gaba Arewa da takwarorinta na sauran yankuna.
Kakakin Shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Majalisar Zartaswa ta Kasa ta kuma amince da rushe Ma’aikatar Bunƙasa Ci-gaban Wasanni tare da mayar da ayyukanta ƙarƙashin Hukumar Kula da Harkokin Wasanni.
Onanuga ya kara da cewa an rushe Ma’aikatar Bunƙasa Ci-gaban Neja Delta da Ma’aikatar Bunƙasa Ci-gaban Kudu maso Gabas.
Ya bayyana cewa za a kafa sabuwar hukumar bunƙasa Ci-gaban Yankuna, wadda za ta ci-gaba da jan ragamar ayyukan ma’aikatun yankunan.