Najeriya Ta Musunta Zargin Hada Kai Da Faransa Domin Haifar Da Matsaloli A Cikin Nijar

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karyata zargin da Shugaban Sojin kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo, inda

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta karyata zargin da Shugaban Sojin kasar Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo, inda ya zargi Nijeriya da haɗa kai da Faransa domin tayar da zaune tsaye a kasar sa. 

A cikin wata sanarwa da Ministan Yada Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya fitar a ranar Alhamis, gwamnati ta bayyana zargin a matsayin mara tushe.

Nijeriya ba ta taba shiga wata yarjejeniya ta boye ko ta fili da Faransa—ko wata kasa—ba domin daukar nauyin hare-haren ta’addanci ko tayar da zaune tsaye a Jamhuriyar Nijar,” inji Idris.

Ministan ya jaddada cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, a matsayin sa na Shugaban kungiyar Hada Kan Yankin Afrika ta Yamma (ECOWAS), ya nuna bajinta ta shugabanci, inda ya ci gaba da budu kofa  ta diflomasiyya da Nijar duk da rikicin siyasa da ake fuskanta a kasar.

Idris ya tabbatar da cewa Nijeriya za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai da kyakkyawar alaka da Nijar.

Haka kuma ya musanta zargin cewa Nijeriya tana yunkurin lalata bututun mai da harkar noman Nijar, ya kira wannan zargin mara tushe kuma mai cutarwa matuka, bisa la’akari da matsayin kasashen biyu makwabta juna na tarihi, wanda komai ya hada su wuri guda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments