Hukumar kare hakkin kwastomomi ta tarayyar Nijeriya ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 220 saboda samun manhajojinsa na Facebook da WhatsApp da laifin keta dokar kare sirrin masu amfani da su a kasar.
A wata sanarwa da Hukumar Nigeria Competition and Consumer Protection Commission (FCCPC) ta fitar ranar Juma’a, ta ce binciken hadin-gwiwa da ta kwashe watanni 38 tana gudanarwa kan yadda manhajojin biyu suke aiki a kasar ya nuna cewa suna kwasar bayanan sirrin mutane tare da yin amfani da su ba bisa ka’ida ba.
Binciken ya gano cewa dokokin Meta suna hana masu amfani da manhajojinsa irin su Facebook da WhatsApp zabi na kin amincewa a kwashi bayanan sirrinsu da kuma mika su ga wasu.
“Baki daya binciken ya amince cewa Meta ya kwashe wani lokaci yana keta dokokin kare sirrin masu amfani da shi a Nijeriya, kuma yana ci gaba da yin hakan,” in ji sanarwar wadda shugaban FCCPC Adamu Abdullahi ya sanyawa hannu.
A baya kasashe da dama sun ci tarar Meta kan keta dokokin kare sirrin masu amfani da manhajojinsa.
Kwanakin baya Tarayyar Turai ta gargadi Meta kan karya dokokin kare sirri.