Najeriya: Gwamnatin Tarayya Da ASUU Sun Gudanar Da Taron Farko, Fiye Da Shekara Guda Da Shigowar Sabuwar Gwamnati

A ranar laraban da ta gabata ce gwamnatin tarayyar Najeriya ta gudanar da zaman tattaunawa ta farko da kungiyar malaman jami’o’i wato ASSU don kaucewa

A ranar laraban da ta gabata ce gwamnatin tarayyar Najeriya ta gudanar da zaman tattaunawa ta farko da kungiyar malaman jami’o’i wato ASSU don kaucewa barazanar yajin aiki.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa an gudanar da taron ne a ma’aikatar ilmi na gwamnatin tarayya a Abuja, kuma tawagar gwamnatin Tarayya a taron sun hada da ministoci biyu masu kula da al-amuran ilmi a kasar wato Tahir Mamman ministan ilmi da kuma karamin ministan ilmi Yusuf Sununu.

Har’ila yau da wasu jami’an gwamnatin tarayya da suke tare. Sannan a bangaren kungiyar ASSU kuma, shugaban kungiyar Emmanuel Osodeke tare da tawagarsa ne suka wakilci ASSU a taron. Kuma an fara shi da misalign karfe 4.30 na yamma, ba tare da halattar yan jaridu ba.

Osodeke ya fadawa kafafen yada labarai bayan taron kan cewa sun tattauna batutuwa da dama daga cikin akwai batun warware al-amuran da suke addabar kungiyar tun  gwamnatin da ta shude. Kuma suna fatan gwamnatin tarayyar za ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa kungiyar bata sake komawa cikin yajin aiki ba.  A bangaren gwamnatin tarayyar kuma ministan Ilmi Tahir Mamman ya bayyana cewa gwamnati za ta dubi bukatun malaman makarantar kuma zata dauki matakan da suka dace don warware su da gaggawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments