Fadar Shugaban Kasar Nijeriya, ta yi watsi da rahoton baya-bayan nan da kwamitin hulda da kasashen wajen Amurka ya fitar, wanda ya kafa hujja da amincewar majalisar dokokin kasar, na zargin kakaba wa wasu kiristoci takunkumi a kasar.
Mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa, Daniel Bwala, ya bayyana rahoton a matsayin wanda ba shi da tushe da makama, yana mai jaddada cewa; tun bayan lokacin da Shugaba Tinubu ya dare kan kujerar mulki a ranar 29 ga Mayun 2023, al’amuran cin zarafi, musamman ta fuskar addini suka yi matukar ja da baya.
Bwala, ya yi wannan furuci ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, wato na D; yana mai jaddada cewa, gwamnatinsu mai ci yanzu; ta himmatu wajen kokarin daidaita addinai a matsayin abu guda.
“Gwamnatin Bola Tinubu, koda-yaushe na kokarin bai wa addinai muhimmanci na musamman. Tun daga ranar 29 ga Mayun 2023, daidai lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau kan karagar mulki, ba a taba samun wasu matsaloli na tsananta wa Kiristoci a ko’ina a fadin wannan kasa ba”, kamar yadda ya rubuta.
Ya jaddada cewa, Nijeriya ta kasance kasa mai dauke da addinai daban-daban, sannan a kowane lokaci gwamnati na kokarin samar da zaman lafiya a tsakanin wadannan addinai.
Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci.