Najeriya: An Yi Kira Ga Shugaba Tinubu Da Ya Sa A Binciko Naira Biliyan 57 Da Su Ka Bace A Ma’aikatar Jin Kai Da Agaji

Hukumar nan mai sa ido akan hakkokin tattalin arziki wacce aka fi sani da ( SERAP)  a takaice ce ta yi kira ga shugaba Ahmad

Hukumar nan mai sa ido akan hakkokin tattalin arziki wacce aka fi sani da ( SERAP)  a takaice ce ta yi kira ga shugaba Ahmad Bola Tunubu da ya umarci ministan shari’ar kasar Mr. Lateef Egbemi  (SAN) da kuma hukumomin dake fada da cin hanci da rashawa na kasar da su bude bincike akan yadda kudaden da su ka kai Naira biliyan 57 suka bace, ko kuma aka sace a ma’aikatar Jin kai da agaji da fada da talauci a shekarar 2021.

A makon da ya wuce ne dai ofishin babban akawu na kasa ya fitar da alkalumma akan yadda wadannan kudaden su ka bace a karkashin ma’aikatar agaji da jin kai a gwamnatin da ta shude.

Rahoton babban akawun na kasa ya kuma bayyana cewa kudaden da aka ce an fitar da su domin  bayar da kayan agaji a zamanin da ake fama da cutar “Covid-19” an riya cewa an aike da su zuwa Kano, Zamfara, da jihar Abia, sai dai kuma da aka bi diddigin wadannan jahohin ba a iya gano inda su ka shiga ba.

Hukumar ta ( SERAP) ta kuma ce duk wanda ake garzi yana da hannu a waccan badakalar ya kamata ya fuskanci shari’a matukar aka tabbatar da kwararan dalilai. Haka nan kuma ya zama wajibi a mayar da kudaden da za a kwato zuwa asusun kasa.

Har ila yau, wannan hukumar ta kira yi shugaban kasar ta Najeriya da ya  yi amfani da kudaden da za a kwato domin cike gibin da ake da shi a kasafin kudi na 2025.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments