Na’im Kassim: Za Mu Sami Nasara Akan Abokan Gaba

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa; Kungiyar za ta sami nasara akan abokan gaba. Sheikh Na’im Kassim wanda yake  mayar da

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa; Kungiyar za ta sami nasara akan abokan gaba.

Sheikh Na’im Kassim wanda yake  mayar da jawabi akan sakon da mayakan na Hizbullah su ka aiko masa daga filin daga a matsayin mubaya’a gare shi, ya ce; ( A cikin sakon naku) na ga yadda ku ka yi imani da batun ‘yanto da Kudus da kasarmu da take a karkashin mamaya. Haka nan kuma yadda kuke kaddamar da jinanenku da sadaukar da shi, kuna gina rayuwar gaba ta zuriya mai zuwa da kuma kare kasarmu. Dukkanin alkairan suna gudana a hannunku.

Sheikh Na’im Kassim ya kuma ambaci ayar kur’ani mai girma da take cewa:  Sai dai manzon Allah da wadanda su ka yi imani a tare da shi, suna yin jihadi da dukiyarsu da kuma kawukansu, wadannan su ne wadanda dukkanin alhairai suke a tare da su, wadannan su ne wadanda su ka rabauta.”

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma bayyana mayakan na kungiyar Hizbullah da cewa su ne; ma’abota karfi wadanda su ka nutse a cikin kaunar Allah, shi kuwa ya yi musu madadi da haskensa. Wadanda suke yin salla, sai karfin da suke da shi ya karu, su ka harba makamai masu linzami da jirage marasa matuki akan makiya da suke girgiza abokan gaba.

Har ila yau Sheik Na’im Kassim ya kuma ce; Zan kasance a tare da ku akan tafarkin Amintaccen sakatare, shahid sayyid Hassan Nasrallah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments