Kungiyar mutanen morocco masu goyon bayan Falasdinawa sun yi allawadai da gwamnatin kasar wacce ta amincewa wani jirgin ruwn HKI ta tsaya a tashar jiragen ruwa na kasar don kara mai da kuma samun abinci.
Kungiyar ta bayyana cewa wannan abin kunya ne ga musulman kasar Morocco wadanda yakamata su katse hulda da HKI, saboda kissan kiyashin da take a Gaza.
Labaran ya kara da cewa abinda gwamnatin kasar Morocco ta yi, ya sabawa kudurorin MDD dangane da yakin da ke faruwa a gaza.
Ha’ila yau ya sabawa hukuncin kotun kasa da kasa ICC dangane da yakin da ke faruwa a gaza. Sannan abin kunya ne ga musulman kasar Morocco.