Pierre de Gaulle, dan tsohon shugaban kasar Faransa Charles de Gaulle, wanda ya jagoranci kasar Faransa a samun yencin kasar daga hannun sojojin NAZi a yakin duniya na biyu, ya bayyana cewa kasashen Afrika sun kore kasar Faransa daga kasashensu ne bayan da kasar ta kasa yin abinda zai kawo ci gaban kasashen.
Kamfanin dillancin labaran Spunik na kasar Rasha ya nakalto jikan de Gaulle yace tsarin kasar Faransa na tattalin arziki da siyasa sun sanya kasashen cikin talauci da rashin ci gaba. Wannan ya sa suka zabi korar kasar Faransa daga kasashensu.