Mutane fiye da 30 ne aka tabbatar damutuwarsu a jiya Laraba a Abubja babban birnin tarayyar Najeriya sanadiyyar bindigan da wata motar daukar iskar gas ta yi a kan gadar Karo da misalign karfe 7:15 a jiya Laraba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hatsarin na jiya ya aukune a dai dai lokacinda direba wata motar dakon mai ta Burma kan wasu ababen hawa a kan gadar Karu dake kan hanyar Abuja-Keffi, sannan ta yi bindiga wanda ya tarwatsa wuta kan motocin da ta tsarewa hanya da dama daga cikin motocin su kuma da wuta kuma mazauna cikinsu sun kasa fita.
Ya zuwa yanzu dai jami’an kwana-kwana da kuma majiyar asbitoci a Asokoro da Asbitin kasa sun tabbatar da mutuwar fiye da 30 sannan wasu da dama suna jinya.
Bayan bayan hawa shugaba Bola Ahmad Tinubu kan shugabancin kasar a watan Mayun shekara 2023 dai an yi hatsarin motocin daukar makamashi har sau a kalla 30, inda mutane kimani 500 suka rasa rayukansa sanadiyyar hakan.
A cikin yan makonni da suka gabata gwamnatin ta hana amfani da manyan-manyan motocin dakon mai masu daukar lita miliyon 60 saboda yawan hatsaron da suke yi.
Iran Press ta tattara bayanai da suka nuna cewa daga shekara 2009 zuwa watan maris na shekara ta 2025 an yi hatsurra tankuna daukar makamashi har 171 a kasar wanda ya lakume rayukan mutane 1,643. Na karshe kafin na jiya larabawa shi ne wanda ya kashe mutane 150 a jihar Jigawa a cikin watan Octoban shekarar da ta gabata.