Munanan Hare-haren Da HKI Take Kai Wa Lebanon Sun Cika Kwanaki 14

Jiragen yakin HKI sun kai munanan hare-hare tun daga daren jiya har zuwa safiyar yau Lahadi a yankin Dhahiya-al-Junub, wanda aka bayyana da cewa, shi

Jiragen yakin HKI sun kai munanan hare-hare tun daga daren jiya har zuwa safiyar yau Lahadi a yankin Dhahiya-al-Junub, wanda aka bayyana da cewa, shi ne mafi muni a cikin kwanaki 14.

A daren jiya din jiragen HKI sun kai hari akan hanyar da take hada filin saukar jiragen sama na “Rafiqul-Hariri’ da cikin birnin Beirut. Harin ya yi sanadin lalata hanyar da kuma wasu gidaje da cibiyoyin kasuwanci da cibiyoyin kiwon lafiya.

Masu aikin agaji sun ambaci wahalhalun da suke fuskanta da shi ne yadda jiragen HKI suke jefa abubuwa masu fashewar gaske da hakan yake hana su ceto da mutanen da aka rutsa da su.

Ya zuwa yanzu adadin mutanen da su ka yi shahada a Lebanon sun haura 2000, haka nan kuma wani adadin mai yawan gaske na mutane sun jikkata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments