Mukaddashin Ministan Harkokin Waken Kasar Iran Yana Rasha Don Halattar Taron Kungiyar BRICS

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bkiri Kani ya isa birnin Nizhny na kasar Rasha don halattar taron ministocin harkokin waje na kungiyar BRICS

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bkiri Kani ya isa birnin Nizhny na kasar Rasha don halattar taron ministocin harkokin waje na kungiyar BRICS a yau litinin.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa Ali Bakiri Kani ya sami tarbar jakadan kasar Iran a kasar Rasha da kuma wasu jami’an ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha.

A jawabin da ya gabatar jim kadan bayan isarsa kasar Rasha, Bakiri Kani ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko na taron ministocin harkokin wajen kasashen BRICS tun bayan da kasar Iran ta zama cikekkiyar mamba a cikinta. Ya kuma kara da cewa kungiyar BRICS dai itace kungiyar tattalin arziki mafi girma a duniya wace bata karkashin kasashen yamma.

Ya kuma kara da cewa samuwar kasar Iran a cikin wannan kungiyar yana nuni zuwa ga matsayi da girman kasar a duniya. Sannan Shahid Raisi shi ne dalilin shigar kasar Iran wannan kungiyar mai muhimmanci ta Brics.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments