Motocin Buldoza Suna Ta Rusa Gidajen Falasdinawa A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur-

Kungiyar Hamas ta bada sanarwan cewa gwamnatin HKI a yankin yamma da Kogin Jordan tana rusa gidajen Falasdinawa a sansanin yan gudun hijira na Nur- Ashamsh, a ranar farko ta watan Ramadan mai alfarma.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Nihad Ashawish shugaban kwamitin mai kula da sansanin yan gudun hijirar yana fadar haka a jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa a jiya Asabar ce motocin Buldoza na HKI suka shiga unguwar Almanshiya suka rusa gidajen wasu Falasdinawa, sannan suka bata hanyoyi a unguwar.

Kamfanin dillancin labaran Abadulu na kasar Turkiya ya nakalti Ashawish yana cewa, sojojin HKI su kan tilastawa Falasdinawa fita daga gidajensu sannan su rusasu a gabansu. Tare da umurnin su fice daga yankin su je inda suka ga dama.

Hamas ta kammala da cewa da wannan aikin zamu fahinci cewa gwamnatin HKI tana son kara korar Falasdinawa daga kasarsu, musamman daga yankin yamma da kogin Jordan.

Kungiyar ta bukaci MDD ta dauki matakan da suka dace don hana yahudawan mamayar karin gidajen Falasdinawa a arewacin yankin yamma da Kogin Jordan.

A jiya Asabar kwanaki 21 cur Kenan gwamnatin HKI take rurrusa gidaje da lalata hanyoyi a garuwan Falasdinawa dake yankin yamma da kogin Jordan musamman garuruwan Tulkaram, da Jenin.

Majiyar asbitoci a yankin yamma da kogon Jordan sun bayyana cewa daga lokacin zuwa yanzu sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 64 sannan wasu dubbai an koresu daga gidajensu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments