Ministocin Tarayyar Turai Sun yi Tir Da Karuwar Hare –Haren Da Yahudawa Ke Kai wa Falasdinawa

Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke

Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke kai wa falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan da isra’ila ta mamaye kuma yake kara ci gaba fiye da kowanne lokaci a baya,

Sanarwar ta fito ne daga minsitocin kasashen birtaniya, jamus , faransa da kuma italiya inda manyan jami’an diplomsiyarsu suka bayyana hare-haren a matsayin mataki ne na tada fitina da kuma ta’addanci.

Haka zalika sun yi kira ga fira ministan isra’ila Benjamin na tanyaho da yayi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa karakshin dokokin kasa da kasa, kuma ya kiyaye hakkin falasdinwa dake zaune a bangarorin da aka mamaye.

Daga karshe sun yi kira ga gwamnatin isra’ila da ta sake siyasarta, kuma sun nuna rashin amincewar su da duk wani mataki na hadewa ko na zahiri , da kuma manufofin ci gaba da gina matsungunann yahudawa  da suka sabawa dojojin kasa da kasa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments