Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Iran Da Rasha Sun Tattauna Kan Rikicin Yankin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da twakaransa na kasar Rasha Sergei lavrov inda suka mayar da hankalin kan

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya tattauna ta wayar tarho da twakaransa na kasar Rasha Sergei lavrov inda suka mayar da hankalin kan batutuwan da suka shafi yankin dama na kasa da kasa

 Ma’aikatar harkokin wajen kasar iran ta bayyana cewa Iraqchi ya jaddada game da muhimmancin zaman lafiya a yammcin Asiya lokacin da yake ishara game da rikicin baya bayan nan  da ya faru tsakanin Pakistan da Afghanistan,

Da ya koma bangaren batun falasdinu kuma Araqchi ya soki matakin da Amurka da kasashen turai suka dauka a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya na gabatar da daftarin kuduri na neman a tilasta tura dakarun kasa da kasa zuwa yankin gaza na falasdinu, yace wannan kuduri yayi hannun riga da ginshikan yanci da kuma hakkin kasa ta zaba ma kanta makoma,

Ana san bangaren lavrov yayi maraba da tattaunawar tasu kuma yace rasha a shirye take ta ci gaba da yin aiki tare da Tehran da kuma tuntuba kan batutuwan da suka shafi yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments