Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Masar Abdulatty donga ne da shirin nukliyar kasar Iran da kuma al-amuran gabasa da tsakiya musamman Gaza.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kasar Masar ta zama mai shiga tsakanin Iran da kasashen yamma dangane da shirin Iran na makamashin nuliya. Haka ma dangane da yaki a Gaza, kasar tana taka rawa don ganin an kawo karshen yakin da kuma shigo da abinci cikin cikin Gaza.
Kasashen Iran da Masar dai suna kai kawo tsakanin kasashen musulmi da kuma kasashen larabawa don don dakatar da wannan kissan kiyashin da ke faruwa a Gaza.
A cikin yan kwanakin da suka gabata, HKI tana kai hare-hare maso zafi a kan mutanen Gaza. Wanda ya tilastawa da dama kauracewa birnin birnin.
Dangane da shirin nukliyar kasar Iran kuma Iran tana kai ruwa rana tsakaninta da kasashen Turai da Amurka kan shirin Nukliyar kasar da kuma kokarin da kasashen E3 suke yi na sake fafrfado da takunkuman tattalin arzikin da MDD ta dorawa kasar kafin yarjeniyar JCPOA..