Minista mai kuma da harkoki da cigaban mata ta kasar Zimbabwe Monica Mutswangwa,wacce ta gana da mataimakiyar shugaban kasar Iran akan sha’anin mata ta ce; Goyon bayan da Iran take bai wa gwgawarmayar al’ummar Zimbabwe, ya sake karfafa alakar kasashen biyu.
Monica Mutswangwa ta kuma yi suka akan yadda kasashen turai su ka kakabawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran takunkunman da ba su da halarci, kuma na rashin adalci da hakan yake yin matsin lamba ga rayuwar mata.
A nata gefen, mataimakiyar shugaban kasar ta Iran Inshiyeh Khaza’ali ta bayyana cewa; Tarihin kasashen biyu wanda yake da alaka da kin jinin mulkin mallaka ya taka rawa wajen bunkasa alakar dake tsakaninsu.
Har ila yau mataimakiyar shugaban kasar ta Iran ta yi ishara da mawuyacin halin da matan Gaza suke ciki saboda yakin da ake yi, tare da yin kira da a kawo karshensa.