Ministar Jin Dadin Jama’a ta Sudan, Salma Ishaq, ta bayyana cewa Mayakan (RSF) sun kashe mata kusan 300 tare da yi wa 25 fyade a El Fasher, babban birnin Jihar Darfur ta Arewa a yammacin Sudan, a matsayin wani bangare na ayyukan kisan kiyashin da suke aikatawa a yankin.
A ranar 26 ga Oktoba, dakarun RSF sun kwace iko da El Fasher kuma sun yi kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa.
A cikin sanarwar da ta fitar Salma Ishaq, Ishaq ta ce abin da ya faru a El Fasher “ya yi kama da abin da ya faru a El Jeneina a shekarar 2023, amma ba a bankado da kuma yada laifukan da suka faru a El Geneina kamar yadda aka yi a El Fasher ba.” Ta kara da cewa dakarun (RSF) sun aikata fyade sau 25, ciki har da cin zarafin yara a gaban iyayensu mata, kafin daga baya a kashe su.
Ta kara da cewa “mutane kadan ne suka tsira a kan da ke tsakanin El Fasher da Tawila, kafin kashe su an azabtar da su, cin zarafinsu, da kuma fyaɗe.” Ta yi gargaɗin cewa ci gaba da kasancewar RSF a El Fasher “zai haifar da kawar da mutanen Darfur,” tana mai bayyana abin da ke faruwa a matsayin kisa ne na kabilanci da nuna wariya, inda ta zargi wasu kasashe da hannu a cikin lamarin.
Ministar ta kammala da cewa, batun mayakan RSF ba batu ne da za a iya magance shi ta hanyar kira ko hanyoyin diflomasiyya da tattaunawa ba, domin kuwa ba su fahimtar hakan, sai dai hanya ta amfani da karfi kawai, in ji ta.