Ministan Yakin HKI Ya Bada Umurnin A Fidda Tsarin Falasdinawa Daga Gaza Da Zabin Kansu

Ministan yaki na HKI Israel Kant ya umurci jami’an gwamnatin kasar su fidda wani tsari wanda zai bawa falasdinawa damar ficewa daga yankin Gaza a

Ministan yaki na HKI Israel Kant ya umurci jami’an gwamnatin kasar su fidda wani tsari wanda zai bawa falasdinawa damar ficewa daga yankin Gaza a radin kansu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan ya na haka  bi sa umurnin da shugaba Trump na Amurka ya bayar na cewa ‘zai kwace Gaza’. Yace  Palasdinawa a Gaza su na so ko basa so za su bar Gaza, a bisa radin kansu ko kuma da karfi.

Shugaban kasar Amurka yace ya dauki nauyin fidda Falasdinawa daga gaza, don wurin ya zama na yahudawan sahyoniyya kadai.

Wasu masana suna ganin mai yuwa wannan shirin zai kawo karshen zaman lafiyan da aka samu, bayan yaki na watanni 15 da suka gabata.

Kant ya bukaci tsarin ya kasance, kan cewa falasdinawa a Gaza za su fice daga gaza su je ko ina suke a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments