Ministan Yaki Na HKI Yace Sojojin HKI Zasu Ci Gaba Da Zama A Kasar Siriya Har’abada

Minisyan yaki na HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sojojin HKI za su ci gaba da zama a kasar Siriya har zuwa illa masha allah,

Minisyan yaki na HKI Israel Kazt ya bayyana cewa sojojin HKI za su ci gaba da zama a kasar Siriya har zuwa illa masha allah, don kare yahudawan da suke zaunwa a tuddan Golan na kasar Siriya da suka mamaye a yakin kwanaki 6 a shekara ta 1967.

Tashar talabijin ta Presstv TV ta nakalto ministan yakin ya na fadar haka a jiya Talata, a lokacinda ya kai ziyara kan ‘Jabal Sheikh’ wani tsauni mai muhimmanci a fagen tsaro, wanda sojojin HKI suka mamaye bayan faduwar gwamnatin Bashar Al-Asad da yan kwanaki. Da kuma bayan da Abu Mohammed al-Julani  shuga kungiyar Deash ya shiga fadar gwamnati a Damascus.

Jabal sheikh dai yana da tsawo sosai ta yadda ana iya kallon dukkan yankunan da ke kusa da shi a cikin kasar Lebanonn da kuma cikin birnin Damascus babban birnin kasar ta Siriya.

Jabal Sheik dai yana tazarar kilomita 20 kacal daga fadar gwamnatin kasar ta Siriya.

Daga karshe yace sojojin Israila sun dawo kasar Siriya ne, ba ranar da zasu bar fice daga kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments