Ministan Tsaron Kasar Iran Ya Gana Da Shugaba Madoro Na Kasar Venzuela

Ministan tsaro na JMI Burgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya gana da shugaban kasar Venezuela a fadarsa dake birnin Caracas babban birnin kasar kuma sun tattauna

Ministan tsaro na JMI Burgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya gana da shugaban kasar Venezuela a fadarsa dake birnin Caracas babban birnin kasar kuma sun tattauna al-amura masu muhimmanci ga kasashen biyu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a ganawar jami’an gwamnatocin kasashen biyu, shugaba Madoro ya bayyana takaicinsa ga irin halin da Falasdinawa suke ciki a cikin kasarsu da aka mamaye. Ya kuma kara da cewa Falasdinawa sune da nasara daga karshe.

Shugaban ya ce, kasashen duniya suna tare da al-ummar Falasdinu kuma suna fatan nan ba da dadewa ba, zasu sami iko a kan kasarsu bayan wahala da masibu na shekaru masu yawa.

A nashi bangaren Janar Aziz Nasirzade ya bukaci kasashen Iran da Venezuela su kara karfafa dankon zumuncin dake tsakaninsu, su kuma karfafa bibiyar duk wata yarjeniyar da suka cimma a baya don tabbatar da cewa an aiwatar da su.

Kafin ganawarsa da shugaba Madoro dai Janar Nasirzadeh ya gana da mataimakin shugaban kasa kuma ministan manfetur na kasar Venezuela Delcy Rodriguz, inda bangarorin biyu suka jaddada bukatar karfafa danganta ta ko wani bangare tsakaninsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments