Ministan Tsaron Isra’ila Ya Yi Barazanar Mayar Da Lebanon Zuwa “Zamanin Dutse”

Ministan tsaron Isra’ila Gallant ya yi barazanar mayar da Lebanon zuwa “Zamanin Dutse” Ministan a wata ziyara da ya kai birnin Washington ya bayyana cewa

Ministan tsaron Isra’ila Gallant ya yi barazanar mayar da Lebanon zuwa “Zamanin Dutse”

Ministan a wata ziyara da ya kai birnin Washington ya bayyana cewa sojojin Isra’ila suna da ikon mayar da kasar Lebanon “komawa zamanin dutse” a duk wani yaki da za ta yi da kungiyar Hizbullah, amma ya dage cewa gwamnatinsa ta fi son a samar da hanyar diflomasiyya a kan iyakar Isra’ila da Lebanon.

Da yake zantawa da manema labarai, Gallant ya kuma ce ya tattauna da manyan jami’an Amurka “kwana daya bayan” shawarwarin da ya gabatar na gudanar da mulki bayan kammala yakin Gaza, wanda zai hada da Falasdinawa na gida da abokan hulda na yanki da kuma Amurka, amma hakan zai kasance “tsari mai tsawo da sarkakiya. ” inji shi.

Kasashen duniya dai na ci gaba da kiran a dauki matakin siyasa domin kaucewa bude wani sabon babi na yaki a iyakar Lebanon da kuma Isra’ila.

A kwana baya shugaban kungiyar Hizbullah, Sayyid Hassan Nasrallah, ya bayyana cewa ba wani wuri da zai zamo mai aminci dga makamai masu linzami na kungiyarsa idan har Isra’ila ta shiga yaki da kungiyar ta Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments