Ministan Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta zama babbar alamar ta’addanci a duniya
Ministan tsaron kasar Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh, yayin da yake yin Allah wadai da kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi wa al’ummomin Falastinu da na Lebanon a daidai lokacin da kungiyoyin kasa da kasa da tarurrukan kasa da kasa suka yi shiru, yana mai cewa: A yau al’ummar yahudawan sahayoniyya ta zama wata babbar alama ta ta’addancin kasa a duniya.
Birgediya Janar Nasirzadeh ya furta haka ne a ganawarsa da ministan tsaron Jamhuriyar Zimbabwe Uba Muchinguri Kashiri a lokacin ziyararsa a kasar Iran, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu. A cikin wannan ganawar, ministan tsaron na Iran ya jaddada cewa: Dangantakar dake tsakanin Iran da Zimbabwe tana da tushe mai tarihi, kuma ta kasance a ko da yaushe bisa abota da mutunta juna. Ya kara da cewa, a cikin shekarun da suka gabata, kasashen biyu sun sami ci gaba mai kyau a dangantakar dake tsakanin kasashensu.